Spread the love

 

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnatin jihar Zamfara ta ba da sanarwar kama wasu sojoji ɓatagari da aka kama suna ba da bayanan sirri da kuma sayarwa ‘yan t’addan Zamfara  makamai, domin biyan bukatunsu.

Kwamishinan yada labarai na jihar ta Zamfara Alhaji Ibrahim Magaji Dosara ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yiwa manema labarai bayanin cigaba da aka samu game da harkar tsaro a jihar, a ofishin sa dake Gusau.

Ya ce bayanan da suka samu ta hannun ‘yan sandan jihar ya nuna cewa akwai hannun mutane da dama wajen taimaka wa ‘yan ta’addan.

Kwamishinan ya ce, gwamnatin Zamfara ta samu rahoto daga hukumar ‘yan sanda an samun nasarar cafke mutun bakwai da suka dukufa wajen taimakawa ‘yan ta’adda a Zamfara,

Waɗan da aka kama dai sun hada da sojoji da wani likita da sauran mutun biyar da ake zargi da mayar da hannun Agogo baya ta fannin tsaro.

Kamar yan da Kwamishinan ya fada, wanda ake zargi na daya, an kama shi da albarushi 20, lokacin da yake mikawa wanda zai sayi albarushin mai suna Kabiru Bashiru dake kauyen maniya, kuma an samu labarin shi sojan har ya karbi kudi naira dubu dari.

Wanda ake tuhuma na biyu, wanda ya fito daga jihar sokoto, an kama shi da kayan sojoji, da kuma rigar kariya ta soja guda tara,da kuma kakin sojoji kala hudu,da safar hannu ta sojoji kwara hudu, da katin ATM biyu na bankin first bank. An kara samun takardar shedar aiki ta soja, da kuma salula kirar Samsung.

Hakama waɗanda ake tuhumar su ne waɗan da aka kama da laifin sayarwa ‘yan ta’addan albarushi da kuma kayan sojoji, waɗan da suka sawo  daga Lagos zuwa Zamfara, bincike ya nuna cewa masu laifin ‘yan asalin karamar hukumar mulki Zurmi ne.

A tabakin Kwamishinan, yan sanda sun kara cafke wani mutun a dajin Dansadau, inda bincike ya nuna cewa an samu hotunan sa inda yake dauke da bindiga kirar AK 47, da kuma sauran nau’in bindigogi daban daban a gunsa.

Alhaji Ibrahim Dosara ya kara bayyanawa manema labarai  cewa, yan sanda sun kara yin nasarar chafke wani likita a kauyen kamarawa, dake karamar hukumar mulkin Isa, jihar sokoto, wanda ake zargi da samarwa yan ta’addan kayan sojoji, da takalman sojoji, da kuma safar hannu ta sojoji.

Mutun na karshe shima an kama shi da kudi naira N523,000,00, da bindiga kirar gida, da guru da layu masu yawa.

Daga karshe Dosara ya yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da cika alkawarin daya dauka na turo sojoji dubu goma a Zamfara domin yaƙar ‘yan ta’addan da suka ki yarda da shirin sulhu domin zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *