Spread the love

Gwamnan jihar Edo ya ce shi ba zai yi musayar kalamai da gwamnatin tarayya ba kan maganar da ya yi na ta buga sabbin kudin kasa biliyan 60 domin tallafawa kudin da ake rabawa a kasa na watan Maris.

Obaseki ya koka kan halin da kasar take ciki a sha’anin kudi ya ce gwamnatin tarayya ta buga sabbin kudi don cike gibin da aka samu a rabon kudin kasa.

“A lokacin da za mu karbi kudin da ake rabawa jihohi sai da gwamnatin tarayya ta buga sabbin kudi naira biliyan 50 zuwa 60 domin kaurin kudin da za a raba.” a cewarsa.

A jiya Laraba gwamnatin tarayya ta ce maganar da ya fada karya ce bai fadi gaskiya ba, Ministar Kudi Zainab Ahmad ta ce kalamansa abin bakinciki ne domin ba gaskiya ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *