Spread the love

Daga Mukhtar A. Haliru Tambuwal

Hatsarin mota  da ya faru a kan titin Gidan Dare in da wani mai babbar mota da ake kira Kanta ya buge  wani matashi mai suna Anas Abdullahi a jihar Sakkwato wanda yake unguwar Gidan Yamma hakan ya yi sanadiyar rasa ransa da matarsa Nusaiba da dansu anan take.

A bayanin da Managarciya ta samu direban motar Kanta ya tuko motar ne ba birki ya zo ya same su sun dawo daga sallar Tarawihi ya buge su.

Direban motar ya gudu abinsa bayan ya yi wannan karen aiki har yanzu ba a sheda kowaye shi ba, a an yi wa  margayan Sallah kamar yadda addini ya shardanta a ranar Alhamis da safe bayan faruwar lamarin a daren Laraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *