Spread the love

Direbobin Kasuwa dake tafiyar kilomita 100 daga Gusau zuwa Dansadau sun shiga yajin aiki kan karuwar fashi da makami da garkuwa da mutane a yankin.

Babbar hanyar ta zama kufai ba motoci a ranar Alhamis  da direbobin suka dakatar da bin hanyar.

Shugaban kungiyar direbobi ta NURTW a Dansadau Isihu Ticha ya ce yajin aikin domin a karkato da hankalin mahukunta ne a dauki matakin da yakamata a yankin.

Ya ce a kwanannan sai da aka sace wasu direbobi su uku, mahara sun karbe babura 16 a cikin satin nan, garkuwa da mutane da fashi da makami kullum sai an yi.

Ya kara da cewar a jumu’ar data gabata aka harbe direban da ya dauko amarya da wasu mutane da suka tafi daurin aure, direban ya mutu aka tafi da amarya da mutanen a nan kusan garin Mashayar Zaki, haka abin yake akwai bukatar daukar matakin da yakamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *