Daga Aminu Abdullahi Gusau.

A cigaba da kokarin da gwamnatin jihar Zamfara ke yi na kara shinfida hanyar da za ta kara kawo zaman lafiya da samar wa jama’a aikin yi, uwar gidan gwamna Hajiya Aisha Bello Muhammad Matawalle, ta gabatar wa ‘ya’yan kungiyar miyetti Allah ta kasa reshen jihar zamfara su ashirin da takardun kama aiki a matsayin mataimaka na musamman ga gwamna Matawalle.

Wannan ya na kunshe ne a cikin wata takardar bayani wadda sakataren  hulda da yan jarida a ofishin matar ta gwamna Hajiya Zainab Shu’aibu Abdullahi ta sakawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a garin Gusau babban birnin jiha.

Da take yiwa wadanda suka samu mukaman siyasar   jawabi, jim kadan bayan ta raba masu takardun kama aiki, matar gwamnan Hajiya Aisha Bello muhammed Matawalle ta basu tabbacin yin aiki da su kafada da kafada domin kara samun cigaban zaman lafiya da walwala a jihar Zamfara, daga nan ta taya su murnar samun wannan mukamai.

Ta kara da cewa wannan karamcin da mai girma gwamna yayi masu ya yi shi ne domin ya kara ba su kwarin gwiwa bisa irin taimakon da suke yi na ci gaban zaman lafiya a ciki da wajen jiha.

Hajiya Aisha Bello Muhammad Matawalle ta ce a cikin yan kungiyar ta miyetti Allah wadanda suka samu mukaman sun hada da maza da mata domin kowanen su ya samu romon dimokuradiyya.

Da yake jawabi a madadin yayan kungiyar da suka samu wadannan mukamai, shugaban kungiyar  miyetti Allah ta kasa reshen jihar zamfara, Alhaji Tukur Abubakar ya yaba wa matar gwamnan bisa ga irin kokarin da take yi na ganin ta kawo canji mai ma’ana ga fulani, da sauran jama’a, dake a jihar ta Zamfara.

Haka zalika shugaban  kungiyar ya yabawa gwamna Bello Muhammad Matawalle, game da irin goyon bayan da yake ba su, da takai ga har ya basu mukamai na siyasa a cikin gwamnatinsa, domin suma su shiga jama’a a dama harkokin siyasa da su.

“Ina baku tabbacin cewa kungiyar mu zata bada goyon bayan ta, da duk irin hadin kan da ake bukata domin samun nasarar wannan gwamnati, da kuma ci gaban jihar mu ta zamfara”. inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *