Spread the love

 

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Kamar yanda ta saba a duk watan Azumi, gwamnatin Zamfara ta kaddamar da rabon buhun abinci ga marayu da marasa galihu a duk fadin jihar.

Da yake kaddamar da rabon kayan gwamna Bello Muhammad Matawalle ya ce, gwamnati ta sayo nau’in abinci daban daban domin rabawa ga mutanenta, don su samu saukin gudanar da Azumin wannan shekara. Ya kara da cewa kamar yanda suka raba kayan abinci a shekarara da ta gabata wannan shekarar sun nunka har sau biyu.

Matawalle ya ce kayan abincin da aka sawo domin rabawa jama’a sun hada da buhun shinkafa, 60,000, da buhun suga 30,000, da buhun gero, 59,000, da kuma buhun masara 30,000 da buhun wake 10,000, da kuma katon 2000 na madara.

“Haka ma mun samar da shadda har kwara 40,000, da atamfa da dai sauran kayayyaki daban daban, ga marassa galihu domin suma su yi bukin sallah cikin jin dadi da walwala.   Kuma zamu gudanar da ciyarwa ta Azumi a mazabu 2,516, da muke da su a duk fadin jihar.

“Saboda haka ma’aikatar kananan hukumomi da ci gaban al’umma, za ta yi hadin gwiwa da shugabanin kananan hukumomi goma sha hudu da muke da su, domin akara yawan wuraren da za’a ciyar da jama’a lokacin buda baki” inji Matawalle.

A tabakinsa ma’aikatan gwamnati suma za su samu nasu kaso, domin a sauka ka masu cikin wannan watan mai albarka, inda ya bada tabbacin cewa ya ba da umurni ga ofishin shugaban ma’aikata da su tabbatar da sun shirya jadawalin yanda za’a rabawa kowace ma’aikata nata kayan abinci.

“Domin samun saukin yin wannan jadawali na ma’aikatun gwamnati mun wakilta wasu ma’aikatu domin su taimaka nuna, ma’aikatun sun hada da ma’aikatar lamurran addini, da kuma hukumar zakka da wakafi, da kuma hukumar da ke kula da baki a fadar gwamnati.

“Kuma ina kira ga masu hannu da shuni dasu taimaka wa jama’a mabukata, da marayu, da zawarawa, da da dai sauran mutane masu bukata ta musamman dake fadin jiharmu.

“Da ga karshe ina rokon Allah subhanahu wata’ala da ya samu cikin wayanda za su morewa wannan watan, kuma Allah ya kara kawo muna zaman lafiya a jihar zamfara da Najeriya ga baki daya, ya kuma karbi ibadar mu”. a cewar Matawalle

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *