Spread the love
Ramadan: Ahmad Lawan Ya Bukaci Musulmi Su yi Ma Najeriya Addu’a
Daga M. A. Umar, Abuja
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bukaci al’ummar musulmi su ba da karfi wajen kira ga zaman lafiya, son juna da hadin kan kasa a wannan watan na Ramadan mai albarka.
Mai baiwa shugaban majalisar shawara kan aikin jarida, Mista Ola Awoniyi ne ya bayyana hakan a wata takardar manema labarai da ya sanyawa hannu.
Takardar manema labaran tace shugaban majalisar dattawan Lawan Ahmad ya bukaci musulmi da su tuna cewa watan na Ramadan lokaci ne na azumi, tausayi, tsarkake kai da kuma sadaukarwa.
Yace, “Ina bukatar mu  tuna da kasar mu a cikin addu’oin mu a wannan lokaci da muke bukatar shawo kan kalubalen da suka sha mana kai.
“Wannan ya zama muhimmi saboda sanin cewa Allah madaukakin sarki mai tausayi ne, kuma shine mai bada mafita ga dukkan matsalolin dan’adam.
“Ina kira garemu da mu jaddada muhimmancin zaman lafiya, son juna, kyautatawa da hadin kai yayin karantarwar mu a wannnan lokacin.
“Kuma kada mu yi sakwa sakwa da bin ka’idojin kiyaye cutar Korona a yayin da muke gabatar da ibadun mu a wannan wata mai alfarma.
Shugaban majalisar yayi ma al’ummar musulmi fatan gudanar da azumin Ramadan karbabbe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *