Spread the love

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha.

Manema labarai sun samu bayanin hukumar ta kama shi da marecen Talata a Abuja.

Majiya a hukumar EFCC ta tabbatarwa daily trust tsohon gwamnan yana hannun hukumar.

Jami’an sun kama shi bayan da yaki karba gayyatarsu da aka yi masa a ofishinsu dake Garki.

Duk kokarin jin tabakin mai magana da yawun Rochas bai samu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *