Spread the love
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ba da sanarwar ganin watan Ramadan a yau Litinin 12 ga watan Afirilu 2021 wanda ya yi daidai da 29 ga sha’aban 1442 shi ne karshen watan sha’aban.
Sarkin musulmi ya ce a bayanin da aka samu wanda kwamitin ganin wata na faɗarsa da kasa  da kungiyoyin addini suka  tantance ya aminta da ganin abin da ke nuna dukkan musulmi a Nijeriya za su tashi da azumin Ramadana a Talata.
Sa’ad ya ce an samu sahihan bayanai na fitar watan Ramadan a dukan fadin Nijeriya.
Ya yi kira ga musulmai su yi wa kasar Nijeriya addu’a kan matsalolin da take fuskanta kuma a bi sharuddan kariya daga cutar Korona.
Ya nemi mawadata a cikin al’umma su taimakawa mabukata a cikinsu musamman a wannana watan na Ramadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *