Spread the love

 

Abin mamaki; tsoron yaduwar cutar Korona bai  hana nadin Sarautun gargajiya  a fadar Sarkin musulmi ba amma  ta hana yin Itikafi a Azumin wannan shekara.

A matsayinmu na musulmai muna da ikon yin magana a duk sanda aka tabo maganar addinin musulunci.

Mi ya sa Kungiyar koli ta addinin muslunci ‘JNI’ ba ta hana taron siyasa da nadin sarautu da aka yi a fadar Sarkin Musulmi a satin da ya da ya gabata sai ibadar Allah wato Itikafi?

Satin da ya gabata da aka shirya  taro a fadar mai martaba sarkin musulmi, inda aka nadawa manyan mutane Sarauntu dabandaban har guda 20, amman hakan bai zama illa ba sai taron Itikafi a watan Azumin Ramadan don bautawa Allah shi ne za a haramta saboda cutar Korona.

A gaskiya yakamata kungiyar JNI ta gaggauta janye wannan kuduri nata na haramta Itikafi, domin sam baiyi daidai ba.

Yakamata malaman addinin su fito su fadakar a  wannan lamari, domin a duk sanda wata musifa ta sauka abin da yakamata a yi shi ne komawa Allah ba kaurace masa ba.

Duk wannan kalamai na Jama’atu shawara ce take bayarwa ga al’umma da hukumomi kan hana yaduwar cutar Korona, a la’akari da yanda mutane ke mu’amala a yanzu a dukkan fadin Nijeriya wannan shawarar ba a bar dauka ba ce  domin ta ci karo da yanda zahirin lamari ke tafiya.

Managarciya ta zagaya a kasuwa da asibiti da makarantu da wasu wuraren da mutane ke taruwa a jihar Sakkwato za ka samu da yawan  mutane sun dauki an kare da wannan cutar kan haka sun bar daukar matakan kariya.

Da yawan mutane ba za su gamsu da wannan shawarar ba, za su ci gaba da shirinsu na shiga masallaci don gudanar da ibadar in lokacin ya zo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *