Spread the love
Sarkin Musulmi ya ba da umarnin a fara duba watan Ramadan daga Litinin
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ba da umarnin musulmin Nijeriya da su fara  duba watan Ramadan a gobe Litinin 12 ga watan Afirilu 2021 wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban 1442.
Sarkin musulmi a takardar da shugaban kwamitin ganin wata na majalisar Sarkin Musulmi Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid  ya ce duk wanda ya gani ya sanar da hakimi ko uban kasar da yake kusa da shi domin sanar da sarkin musulmi.
Bayanin ya zayyano nambobin da ake iya kira domin sanar da kwamitin ganin wata kamar haka: 08037157100, 07067416900, 08036149757, 08035965322.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *