Spread the love
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Jam’iyyar APC jihar Zamfara ta ce ta shirya tsab domin raba kayan abinci har mota tirela 130, ga ‘ya’yanta da kuma marasa galihu domin fara Azumin watan Ramalana.
Tsohon gwamnan jihar kuma jigon APC ta Zamfara Abdul’aziz Yari Abubakar ne ya sanar da haka, a lokacin da yake  kaddamar da rabon kayan abinci a ofishin jam’iyyar dake Gusau babban birnin jiha.
Yari, wanda ya samu wakilcin Sanata  Kabiru Garba  Marafa ya ce kayan da za’a raba sun hada da Tirela 54 na buhun  shinkafa mai nauyin kilo 50, da Tirela  32  buhun suga mai nauyin kilo 50, da Tirela, 22 na buhun masara , da kuma Tirela  22 ta buhun gero. Ya ce za’a raba kayan ne a fadin kananan hukumomi 13.
“Ko wace karamar hukuma za ta karbi Tirela biyar, wanda sunka hada da tirela biyu ta shinkafa, tirela daya  ta suga, tirela daya ta masara, da kuma tirela daya ta gero, kuma duk wadanda basu samu wannan kason a hakaba su kirani su fada mani.
“Amma ita karamar hukumar mulkin Gusau za mu bata kaso mafi tsoka, kasan cewar wata mai yawan jama’a, inda za’a bata tirela 10, idan muka tada lisaafi zai bamu a dadin tireloli 75” Inji Marafa amadadin Abdulaziz Yari.
Jigon APCn na zamfara ya kara da cewa sauran tirela 55 za’a rabawa marayu, musakai, masu bukata ta musamman, jami’an tsaro, mawaka, ‘yan jarida da ‘yan social media dukansu a jihar Zamfara.
“Jama’a kar ku manta da cewa duk wadan nan kayan abinci jam’iyyar APC ce ta samo su kuma za ta ba mutane, bisa ga la’akari da irin tashin gwabron zabi da kayan abinci ya yi a Najeriya.
“Muna gadiya ga shugabannin jam’iyyarmu na jiha, bisa ga kokarin da sukavyi na ganin mun dunke barakar da ta same mu har muka rasa gwamnati a zaben da ya gabata” inji Yari.
A dan nasa tsokaci, wakilin Sakatariyar uwar jam’iyyar APC ta kasa Sanata Abba Aji ya nuna jin dadin sa ga jigon na APCn a zamfara bisa ga tunanin su na  taimakawa jama’a a lokacin wannan watan mai alfarma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *