Spread the love

A yau ne Assabar uwar jam’iya ta ƙasa ta aiyana a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen shugabanin yanki a arewa maso yamma.

Kafin gudanar da zaɓen aka jiyo madugun Kwankwasiya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso  na ƙorafi kan Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal na yi masu gutsiri tsoma a kujerar mataimakin shugaba na yankin  da aka ba su.

Tambuwal ya ƙaryata zargin na cewa ya sayawa Sanata Bello Hayatu Gwarzo Fom na takarar sai dai  ya ce kowa nada ‘yancin ya nemi kujerar matuƙar ya cancanta.

Sanata Kwankwaso ya yi kalamai masu zafi kan zargin in da ya kira Tambuwal mutum ne  mai gaggawa da rashin iyawa wannan kuskure ne a damar da yake da ita.

Ya zargi hukuma a Nijeriya ta fanshi zaɓensu da aka yi  ne a 2019 dana Sakkwato, “An juye zaɓen ya koma Sakkwato na Sakkwato ya koma Kano” a cewarsa.

Bayan an shigo domin soma zaɓen wasu matasa da ba a san ko suwaye ba suka zo suka hargitsa wurin abin da ya haifar da ɗage zaɓen domin hayaniya ta kaure dole kowa ya bar wurin zuwa jiharsa.

Wasu magoya bayan Tambuwal sun zargi mutanen Kwankwasiya ne suka yi hakan duk da har yanzu gefen bai ce komai a kai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *