Spread the love
Sarkin Gabas na Durbawa Alhaji  Mu’azu Yakubu Durbawa ya cika shekara 7 saman karaga  cikin mutunci da ƙoshin lafiya.
 Sarkin Gabas wanda shi ne uban ƙasar Durbawa na 17, amma kuma shi ne Sarkin Gabas na farko hakan ya sanya shi ƙoƙari matuƙa domin kare mutunci da martabar gidansu.
A shekarru bakwai da Sarki ya yi ya samar da haɗin kai a tsakanin al’ummar yankinsa, abin da ya taimaki yanki wurin haɓakar tattalin arzikinsu da bunkasar cigabansu.
Wannan shekarun  nasa masu albarka ne ga mutanen yankin da Sakkwato gaba ɗaya ganin yanda yake faɗi tashin samar da al’umma ta gari da ƙoƙarin ganin matasa sun zama masu dogaro da kansu ta hanyar yin sana’a ko wani aiki da dokar ƙasa da addini suka  aminta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *