Spread the love

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Najeriya Usman Alkali Baba a zaman sabon mukaddashin  sufetan ‘yan sandan Nijeriya.
Sabon shugaban zai maye gurbin Muhammad Abubakar Adamu wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon wannan shekarar.
Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban kasa Malam Garba Shehu ne ya tabbatar wa da hakan a zantawarsa da manema labarai.
Kafin nadin yana rike da mukamin DIG ne a hukumar ‘yan sanda na  kasa a bangaren bincike masu manyan laifuka.
Mukaddashin dan asalin jihar Yobe ne ya yi digirinsa a jami’ar Bayaro ta Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *