Spread the love
  1. Gwamnonin APC sun kaddamar da gidajen saukar baki  18 da gwamnatin Zamfara ta gina.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC karkashin jagoran cin shugaban kungiyar sanata Atiku Bagudo, sun bude gidajen saukar baki har guda goma sha takwas da gwamnan zamfara Bello Muhammed Matawalle ya gida domin saukar da baki a gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jiha.

Wayan nan gidajen na saukar baki, an gina su ne domin saukar da jiga jigan gwamnati duk lokacin da suka bakunci jihar ta zamfara, hadi da gwamnonin arewa su goma sha takwas, inda ko wane gida an saka sunan jihar da zai wakilta.

Da suke kaddamar da gidajen shugaban kungiyar gwamnonin APC, kuma gwamnan jihar Kabi, Sanata Atiku Bagudo, da shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC, gwamnan Yobe Alhaji Mai Mala Buni, da kuma gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, sun yaba wa gwamna Bello Mohammed Matawallen Maradun bisa ga irin kokarin da yake yi na kawo canji mai ma’ana ga wannan jihar.

Haka ma sun kara da cewa wannan tunanin da yayi na gina wayan nan katafaren gidajen ya kara wa gidan gwamnati kyawo, kuma ga shi gidajen nada kyawon da za’a iya saukar da ko wane irin bako ba tare da anji kunya ba.

Sun kara da cewa gwamna Matawalle mutun ne wanda ko yaushe yana kokarin yaga ya kawo ma jama’ar sa romon dimokuradiya, kuma mutun ne mai son kawo zaman lafiya, wanda ya gina gidajen saukar baki cikin kankanen lokaci.

Da yake yiwa gwamnonin baya ni tun da fari, gwamna Bello Mohammed Matawallen Maradun yace, ya yanke shawarar gina gidajen saukar bakin ne domin ya bada isashen masauki ga jami’an gwamnato cin jihohin Najeriya idan suka kawo masa ziyara, ko kuma in sun shigo domin aiki.

Gwamnan ya kara da cewa, gina wayan nan gidajen saukar baki zai rage irin kudade da gwamnati ke kashewa wajen saukar da su.

Matawalle ya bayyana cewa wayan nan gidajen suna daya daga cikin ayyukan alheri da gwamnati keyi domin ciyar da jiha a gaba.

Gwamnonin dai sun gamsu da irin namijin kokarin da matawalle keyi na kawo ci gaban zamfara da kuma bayar da tsaro ga mutanen sa, inda suka ce cikin shekara daya da rabi ya samar da tsaro fiye da yanda ake can a shekarun baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *