Spread the love

 

Mai martaba Sarkin Musulmi a lahadin nan ya naɗa sabbin sarautu guda 20 ga wasu manyan mutane a Sakkwato da wajenta bayan kwana 22 da naɗa mataimakin gwamnan Sakkwato Alhaji Maniru Muhammad Dan’iya matsayin Walin Sakkwato.

Sarkin musulmi a jawabinsa ya ce sarautun da aka bayar an yi ne samam cancanta ba tare da shigar da  siyasa ba saboda a kara inganta lamurran addini a samu cigaba.

Ya ce bai taba bukin naɗi na mutane masu yawa kamar wannan ba an yi hakan ne domin ƙara bunƙasa masarauta da harkokin addinin musulunci a Nijeriya  musamman taimakawa masu ƙaramin ƙarfi.

Managarciya ta fahimci yanda hankalin mutane a Sakkwato ya dawo kacokam kan harkokin naɗin bayan an naɗa mataimakin gwamna a lokacin da ba a za ta ba, amma su sauran an sanya masu rana da su damar  yin shiri kuma su bayyana a gaban masoyansu a naɗa su cikin fsrinciki da girmamawa.

Hakan ya baiwa masu bibiyar lamurra a jihar hasashen abin da ya dace da hankalinsu, in da wasu ke samarwa kansu kan  zaren tunaninsu da yanken hukuncin sai lokaci ya zo don ya bayyana masu gaskiyar hasashensu, a yayinda wasu suka faɗa cikin ruɗanin tunanin sanin mi ake nufi na ware mataimakin gwamna da yin sarautarsa, ba a gudanar da shagalin  buki ba,  don sun tabbatar dalilin da aka bayar ba shi da muhali da zai  hana bukin naɗi.

Naɗin sarautar da yafi jan hankalin mutane sun hada dana gidan tsohon Sarkin misulmi Ibrahim Dasuki da aka naɗa mutum uku daya daga cikinsu Honarabul Abdussamad Dasuki wanda yake kwamishinan kuɗi kuma makusanci ne  ga gwamna Aminu Waziri Tambuwal har wasu sun fara hasashen Tambuwal zai iya tsayar da shi a matsayin wanda zai gaje shi a 2023 ganin kowane bangare na jihar gudu uku sun samar da  gwamnan Sakkwato, don haka ana iya farawa  da yankin da gwamnan ya fito abin da wasu ke ganin ba zai yiwu ba.

Sarautar Dan malikin Sakkwato ma ta ja hankali ganin  yanda dan siyasa kuma dan kasuwa Aminu Buhari Galadima ya tsara bukinsa cikin tsari da hikima gwanin sha’awa, shi kadai ne Basaraken da ya hau doki a ka yi masa karamar Daba kafin ya tafi gidansa.

Wadan nan sarakuna dukansu sun yi askin sarauta a gidajensu in da masoya suka nuna bajintarsu ta nuna soyayya, abin da ya ja hankalin Managarciya da yin tambayar Wali da aka fara nadawa kafin su  yaushe ne zai yi nasa bukun askin, ko shi tasa sarautar ba ta da aski ne?

Daraktan yada labarai a ofishin mataimakin gwamna   Aminu Abdullahi ya ce askin sarauta ba kowa ke yin sa ba ya dangata da bukatar mutum, “amma ni ban da wata masaniya kan wani aski da za a yi, ban yi tsammanin za a yi ba”. a cewarsa.

Hakan ke nuna Walin Sakkwato da wuya ya yi askin Sarauta kamar yadda wasu Sarakunan suka yi, duk da wasu na ganin kamar zai shirya wata rana da zai yi wannan bukin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *