Spread the love

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana yawan yaran da ba su zuwa makaranta a fadin Nijeriya

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce yawan yaran da ba su zuwa a makaranta a yanzu ya sauka daga miliyan 12 ya koma miliyan 10.3.

Gwamnatin tarayya ta ce shigar masu ruwa da tsaki ne a haujin ilmi ya kawa lamarin rashin zuwan yara makaranta ya ragu.

Babban sakatare a ma’aikatar ilmi ta ƙasa  Sonny Echono, ta faɗi haka a taron ilmi kan kididigar ilmi a ƙasa wanda ya gudana a   Abeokuta, jihar  Ogun.

Ta ce ƙididigar ta bayyana ba dukkan yaran da ke cikin makaranta ne suke ciki da shekarrunsu ba a wasu ɓagarori na Nijeriya.

Ta ce har yanzu akwai tirjiya na zuwan har a Kudu maso Yamma wasu yaran sun bar zuwa makaranta ga matsalar rashin daidaito yara maza sun fi mata yawa a makarantu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *