Spread the love

 

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Ga dukkan alamu ‘yan wasan jihar Zamfara da za su wakilci jihar a wasannin kasa da za’ayi a jihar Edo, watau (EDO 2021), ba za su samu damar yin hakan ba saboda rashin isasshen kudin da hukumar wasanni ta jihar ke fuskanta, sai dai idan gwamnati ta sa hannunta. Kamar yanda bincike ya nuna.

Wannan gasar wasanni da za’a gudanar a jihar Edo, an sanya jadawalin fara ta ne a ranar lahadi 4/4/21, a jihar ta Edo.

Amma har yau ranar jumu’a wadda ita ce ranar da kowace jiha za ta tura ‘yan wasanta, amma su yan wasan jihar Zamfara da shuga banninsu na hukumar wasa ta jihar suna nan suna jiran yanda za ta kaya, ko za su tafi ko kuma akasin haka. Duk da yake sun shirya ma zuwa wajen gasar.

Bincike ya nuna cewa babu wani takamammen shiri da hukumar wasar jihar ta yi domin barin Zamfara zuwa Edo, saboda matsalar kudin da basu samu ba daga gwamnatin jihar ba.

Wasu daga cikin ‘yan wasan da ke dakon jiran susan makomar su, sunyi wa manema labarai bayani, inda suka nuna rashin jindadin su ga gwamnati na rashin ba da kudin gudanar da wannan tafiya mai mahimmanci. Suka kara da cewa ba su taba fuskantar irin wannan koma baya ba.

‘Yan wasan da suka nemi a sakaya sunansu sun ce,” Ba mu ji dadin wannan tsaiko ba, domin gamu a shirye muke muna sa ran mu tsahi zuwa Edo, domin mu wakilci jihar mu wadda muke alfahari da ita amma gashi an barmu da yin tagumi, saboda gwamnati taki ta bada abun da ya kamata domin tafiyar mu”.

Daga nan sai suka yi kira ga gwamnatin jihar ta Zamfara karkashin jagoran cin gwamna Bello Matawalle da ya duba halin da ake ciki ya samar ma hukumar kudin da za su dauki nauyin ‘yan wasa kamar yanda aka saba.

Ana shi bayani kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara Alhaji Ibrahim Dosara ya ce, hakika gwamnati ta shirya duk abun da ya kamata domin taga cewa ta samu wakilci wajen gasar wasannin, ya kara da cewa tun lokacin da ake shirye-shiryen an samarwa ‘yan wasan kayan wasanni daban daban.

Kwamishinan ya ce kowa ne lokaci daga yau din nan zasu tashi zuwa Edo, domin su wakilci jihar su abun alfaharin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *