Spread the love

 

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Matsalar rashin wadatacciyar wutar lantarki da ke addabar karamar hukumar mulkin Kauran Namoda dake jihar Zamfara ya jawo tabarbarewar tattalin arziki da harkokin yau da kullum.

Wannan bayani yana dauke ne a cikin wata takardar bayani wadda sakataren yada labarai na kungiyar “Kaura-Namoda Focus Forum” Comrade Abdurrazak Bello Kaura ya rataba wa hannu kuma ya rabawa manema labari a Gusau babban birnin jihar Zamfara, inda yace karamar hukumar Kauran Namoda ita ce ta biyu ga yawan jama’a a jihar Zamfara, amma abun takaici ko yaushe jama’ar su na zaune cikin duhu, fiye da shekara daya.

Abdurrazak ya ce, yanzu sun riga sun zama babu wanda zai taimaka masu domin magance wannan matsalar, a matsayin su na yan kasa masu bin doka da oda..

Sakataren ya kara da cewa hukumar wutar lantarki ta Kaduna watau (KAEDCO) tasa son rai kwarai da gaske ta yanda take raba wutar lantar kin, ga kwasto momin ta hasali ma mutanen Kaura Namoda.

Abdurrazak ya ce hukumar ta KAEDCO ta kasa bin ka’idar aikin su ga kwasto minsu, “Sun barmu cikin duhu, kuma suna cajin mu kudade ba tausayi, don bamuda zabi game da yanda suke raba muna wutar lantar ki a wajajenmu”.

“Harkokin kasuwancinmu duk sun tsaya cik, don gaskiya yanzu muna cikin yanayi na ban tausayi, game da rashin wutar lantar ki, wanda wannan abun ya iya jawo tabar barewar tattalin arziki da rashin aikin yi ga matasa.” inji shi.

Duk da haka ya yabawa kokarin wasu ma’aikatan wadanda ke yin kokarin cewa an samarwa jama’a isashiyar wutar, ta hanyar maleji da YAN kayan aikin dake nan a garin na Kaura.

“Abun da ma’aikatan na KAEDCO ke yi muna, shi ne za su samar muna da hasken wutar lantar ki can ba a rasa ba, kuma basu dadewa kamar awa daya zuwa awa ukku sai kaga sun dauke wutar, kuma ma sunfi yin hakan idan an kai karshen wata don kawai su karbi kudin wutar. Kuma ya zama dole mu biya don kada a katse muna wutar.

“Idan cabe ya fadi, lalacewar transformer, ko fuse ya katse, da kuma gyaran cable, sai kaga hukumar KAEDCO ta bar mutanen gari da ma’aikatan ta su gyara ba ruwan su”.inji shi.

Ya kara da cewa ana chajin mutane kudin wata ba tare da la’akari da ko sun bada isashiyar wutar ba.

“Suna karbar akalla naira N4,000 ga kuwa ne magidan ci, ba tare da la’akari da cewa bamu cika amfani da wutar ba”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *