Mutane bakwai haɗi da sojoji biyar da ma’aikacin Sibil defens ɗaya ne aka kashe a wani hari da aka kawo kauyukka biyar a karamar hukumar Shiroro jihar Neja.

Sama da mutane 10 aka yi garkuwa da su da sace babur bakwai sun kone wasu motocin sojoji a lokacin da suka kai harin

Garuruwan da suka kai hari sun haɗa da  Allawa, Manta, Gurmana, Bassa da Kokki.

A bayanin da aka samu harin an fara a Laraba har Alhamis da safe da yawan mutane sun samu rauni suna karbar magani a cibiyoyin lafiya a karamar hukumar Shiroro.

Maharan sun zo garin Allawa a wurin da jami’an tsaro suke da misalin 2 na daren alhamis suka bude masu wuta anan take suka kashe soja biyar da jami’in tsaron sibil difens da ‘yan sa kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *