Spread the love

Ministar kudi da kasafi da tsare-tsare ta Nijeriya Hajiya Zainab Ahmad ta bayar da kididdigar cewa gwamnatin tarayya za ta kashe biliyan 296 ga allurar rigakafin Korona a 2021 da 2022.

Ta kuma sanar cewa kasafin kudi na musamman kan sayen kayan aikin samar da tsaro da allurar Korona har yanzu bai kammala ba.

Ahmad ta furta hakan ne a lokacin da take magana da manema labarai a fadar gwamnatin tarayya bayan kammala zaman majalisar zartarwar kasa da ya gudana a karkashin kulawar mataimakin shugaban kasa Osinbajo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *