Spread the love
Gobarar kasuwa: Gwamna Badaru da Bagudu sun  ba da tallafin miliyan 40 ga ‘yan kasuwar Katsina
 Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya bayar da gudummuwar naira milyan ashirin ga mutanen da iftila’in gobara ya afka musu a babbar kasuwa ta jihar katsina.
Gwamnan ya bayyana gudummawar ne a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari tare da takwaran sa na Jihar Kebbi Alhaji Abubakar  Atiku Bagudu wanda shi ma ya ba da makamanciyar gudummuwar ta miliyan 20 ga  ‘yan kasuwar.
Da yake jawabi, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya ce sun zo jihar Katsina ne dimin su jajantawa Gwamnan da kuma yan kasuwar da suka yi asarar kaya na miliyoyi sakamakon gobarar da aka yi satin da ya gabata.
A satin da ya gabata ne kaddarar wutar gobara ta tashi a  kasuwar ta Katsina in da aka samu hasarar dimbin dukiya.
A kalaman Gwamnan na Kebbi ya jajantawa ‘yan kasuwar da suka tabka hasara da roka masu Allah ya mai da masu mafificin alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *