Spread the love

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan yada labarai Malam Garba Shehu ya yi bayanin dalilin da ya sanya shugaban kasa bai mika mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo kafin ya tafi London ba.

Ya yi magana da gidan talabijin na Chanels ya ce shugaban bai bayar da mulki ba ne domin ba wani dadewa ne zai yi ba.

Shugaban kasa zai iya aikinsa a duk in da yake domin tsarin doka ya ce sai in shugaban kasa ya yi kwana 21 ko fiye sannan ne zai iya ba da mulki ga mataimaki.

Ya ce shugaban kasa yana da karfin jiki kawai ya tafi ne domin  a duba lafiyarsa, wannan tafiyar ba ta gaggawa ba ce kawai ya tafi ne domin a duba jikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *