Spread the love
Daga M. A. Umar, Abuja
Ofishin shugaban majalisar dattawa ya yi watsi da wani sakon yanar gizo a tiwita da wani mai suna Kwamared Mayor yayi inda ya jingina wasu kalaman karya ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.
A sakon na tiwita, an ruwaito shugaban majalisar dattawan yana cewa ba zai damu ba idan har za’a yi ma kundin tsarin mulkin kasar nan kwaskwarima don barin shugaban kasa ya zarce wa’adi uku muddin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bukatarsa ta cigaba da mulki bayan shekarar 2023.
Da farko mun so muyi banza da wannan labarin kanzon kuregen, musamman ganin cewa ba sabo ba ne, an fara aikawa da shi ne shekaru biyu da suka wuce a ranara 27 ga watan Maris na 2019.
Amma ya zama wajibi mu karyata sakon a hukumance ganin cewa ana cigaba da aikawa da shi a shafukan sada zumunta na soshiyal mediya.
Bayanin hakan na kunshe ne a takardar manema labarai, da mai taimakawa shugaban majalisar a kan jaridu, Mista Ola Awoniyi a yammacin littinin din nan a Abuja.
Ya kara da cewar muna masu fada karara cewa shugaban majalisar dattawa bai taba fadar wannan magana ba kafin ko bayan 2019
A yanzu masu baza labaran karya sun dawo da zagayawa da tsohon sakon na tiwita wanda wasu maketata suka yi.
Kundin tsarin mulki na shekarar 1999 yana da matsaya mai karfi akan wa’adin mulkin shugaban kasa wadda mafi yawan yan Najeriya suke goyon baya.
Sashi na 137(1)b ya samar da cewa mutumin da aka zaba a matsayin shugaban kasa har sau biyu ba zai cancanta a kara zaben sa a wannan mukamin ba.
Shugaban Majalisar dattawa bai taba ganin matsalar wannan tanadi na tsarin mulki ba, kuma a ko yaushe ya tsaya da yarda akan wannan tanadin.
Za’a iya tuna cewa a shekarar 2006 a lokacin Ahmad Lawan yana dan majalisar dokoki ta tarayya majalisar ta ki amicewa da yunkurin gayaran wannan sashi na kundin tsarin mulki dan kara wa’adin mulki  shugaban kasa.
A lokacin majalisar dokoki ta tarayya ta dauki matakin a bisa la’akari da ra’ayin da bukatar mafi yawan Najeriya.
Don haka, zai zama shirme a yi tunanin Ahmad Lawan zai zama jagora akan abinda ba zai taba nasara ba idan aka kara kokarin yin sa.
Matsayin shugaban majalisar shine na tsayawa akan tanadin tsarin mulki akan wa’adin mulkin shugaban kasa da yan Najeriya suka yarda kuma suka amince da shi.
Don haka muna kira ga jama’a da suyi watsi da wannan tsohon laabarin kanzon kuregen da aka danganta da shugaban majalisar dattawan, wanda wasu marasa son zaman lafiya suka dawo da yada shi a halin yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *