Spread the love
Hankalinmu ya karkato da wani labarin ƙarya da aka riƙa yaɗawa a kafofin sada zumunta cewa mun dakatarda tsohon gwamnan Neja ɗaya daga cikin mambobin kwamitin amintattu na PDP waton Mu’azu Babangida Aliyu daga cikin jam’iyarmu.
Ba za mu tsaya sa’insa da mutanen social media ba, amma dole ne mu sanar da magoya bayan jam’iyarmu a jihar Neja kar a ruɗar da su ga lamarin da ba gaskiya.
Abin da yake gaskiya tsohon gwamna ba a dakatar da shi ba a matakin mazaɓarsa.
Mutanen da suke yaɗa wannan labarin don su kawo rashin haɗin kai a tsakanin magoya bayan jam’iya a jihar.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyar a yankin Neja Suleman Muhammad ya fitar da bayanin ya ce mutane su fita batun labarun ƙanzon kurege.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *