Kungiyar likitoci mazauna gida(Residents Doctors) sun yi matsayar fara yajin aikin na sai baba ya gani daga 1 ga watan Afirilu 2021 matukar gwamnati ta ki gaggauta biya masu bukatunsu.

Wannan matsayar an cimma ta ne a wani zaman na musamman da shugabannin kunngiyar suka yi a ranar Assaabar data gabata cikin asibitin kasa dake Abuja a lokacin da suka zauna domin duba wa’adin da suka bayar na a duba lamurran likitoci da walwalarsu da kayan kiyon lafiya da horaswarsu.

An yanke albashinsu a 2014 da 2015 da 2016 a asibitocin tarayya da jihohi bayan aminta da tsarin biyan albashi da NARD suka yi a farko, yana cikin bukatunsu da suke son a warware nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *