Spread the love
Daga M. A. Umar, Abuja.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya aike da sakon fatan alheri ga tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu a bisa cikar sa shekaru 69 da haihuwa.
Lawan ya bi sahun iyalai, abokai da abokan tafiyar siyasar jigon na jama’iyar APC wajen taya sa murnar zagayowar wannan rana cikin koshin lafiya da karkashi.
Yace, “ina taya mai girma Asiwaju Tinubu murna a bisa wannan lokaci na farin ciki.
“A sama da shekaru talatin, Asiwaju Tinubu wanda yake jagoran jagorori, masanin tsarin siyasa kuma masanin iya mulki ne ya taka gaggarumar rawa a siyasar Najeriya inda ya inganta rayuwar mutane da dama ya kuma assasa siyasar dimokaradiyya.
Ola Awoniyi, mai baiwa shugaban shawara a bangaren jarida ya aike da sakon yau ga manema labarai, inda ya cigaba da cewar, “Nasarorin da ya samu da kafa tubalin cigaban jihar Legas a lokacin da ya zama gwamnan jihar na farko a wannan jamhuriyar ta hudu ya sama masa kyakykyawan gurbi a tarihin jihar.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa ya cigaba da kasancewa shahararre a fagen siyasa duk da yabar ofis shekaru 14 da suka wuce.
“Jagaban na Borgu, wanda daya daga cikin wadanda suka kafa jama’iyar mu mai albarka ta APC, ya kasance jajirtacce tare da sauran shugabannin mu wajen saisaita jama’iyar mai mulki akan hanyar cigaba don bunkasa dimokaradiyyar mu da cigaban kasar mu.
“Asiwaju Tinubu ya cigaba da kasancewa jajirtarce akan hadin kan kasar nan tare da yardar sa akan makomarta na bunkasashiyar kasa da jama’ar ta suke cikin farin ciki da walwala duk da kalubalen da ake fuskanta”.
Shugaban majalisar yayi ma tsohon gwamnan fatar karin shekaru masu yawa a cikin koshin lafiya da kara yi ma al’umma hidima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *