A kiran da ake yi matasa su shiga harkokin siyasa a zaɓen shugaban ƙasa da wasu zaɓukka a 2023 ɗan tsohon shugaban ƙasa  Olujonwo Obasanjo ya yi kira Gwamnan Kogi ya nemi takarar kujerar shugaban ƙasa a 2023.

Olujonwo ya bayyana Bello matsayin wanda ake sa rai kansa don haka yakanata ya nemi tsayawar don samar matasa wuri.

Obasanjo ya yi wannan bayanin ne a Abuja bayan ya ziyarci gwamnan ya ce matasa a ƙasar nan an barsu baya tsawon lokaci duk da gudunmuwar da suke bayarwa a wurin zaɓe amma an ƙi ba su dama a wurin zartar da hukuncin siyasa.

Managarciya ta fahimci Yahaya Bello ya fito kuma da gaske yana son ya mulki ƙasar Nijeriya abin jira a gani ko zai samu tikitin tsaya na jam’iyarsu ta APC lokaci ne zai amsa wannan.

Ya ce kuzarin da matasa suke da shi ba wanda ke shakkunsa musamman waɗanda ke ganiyar 35 zuwa 45.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *