Spread the love

Jam’iyar APC mai adawa a jihar Sakkwato ta fitar da wani bayani da ta rabawa manema labarai a Sakkwato in da ta yi kira ga gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da ya rabawa ‘yan kasuwar da suka hadu da ibtila’in gobara kudin da suka samu na gudunmuwa daga wasu manyan mutane  a ciki da wajen jihar Sakkwato.

Alhaji Isah Sadik Achida shugaban riko na jam’iyar ne ya fitar da bayanin ya ce “In muna iya tunawa a watannin da suka gabata wutar gobara ta lakume wasu shaguna a babbar kasuwar Sakkwato, Gwamna Tambuwal ya bayyana kudirin sake gina shagunan cikin wata biyu, alkawalin da har yanzu bai cika ba, lamarin da ya kara jefa ‘yan kasuwar cikin rudanin da yafi na lokacin da lamarin wutar ya faru.” a cewar Achida.

Ya ci gaba da cewa har yanzu ba ta baci ba suna kira ga gwamnatin Sakkwato ta duba yiwuwar raba kudin gudunmuwar da aka baiwa ‘yan kasuwar wanda wasu manyan mutane suka bayar don tausayawa da rage masu zafin hasara da suka yi fitar da kudin a yanzu  abin dubawa ne ganin yanda watan Azumin Ramadan  ke karasowa domin lokaci ne da ‘yan kasuwa ke yin hada-hadar kasuwancinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *