Shugaban kamfanin Man fetur na kasa NNPC Mele Kyari ya ce a halin yanzu tallafin man fetur yana lakume tsakanin biliyan 100 ko 120 a kowane wata.

Kyari ya sanar da hakan a lokacin da yake karba tambayoyi ga manema labarai a Abuja.

Wannan bayanin nasa zai kara rikitar da mutanen kasa saboda maganar janye tallafin man fetur  da aka rika yi a wannan gwamnati ta shugaba Buhari.

Shugaban ya ce nauyin ya yi masu yawa yanda ake sayar da litar Man kan 162.

Ya ce gwamnatin Nijeriya tana biyan wahalhalun zuwan Man ne wanda in aka lissafa a kowace lita kudinta zai kama 234, amma gwamnati ta yi iya kokarinta ana sayar da Man  162 a kowace lita.

Ya ce matukar kasuwa ta matsa za a barta ta yanke hukuncin yadda farashin Man zai kasance a kasar Nijeriya.

Ya kara da cewar gwamnatin na duba yanda karin farashin man zai zama mai alfanu ga mutanen Nijeriya.

Managarciya ta kasa fahimtar abin da wannan gwamnati ke nufi da talakan Nijeriya ba ta fada masa gaskiya yanda zai fahimci lamari, a farkon kara farashin man fetur a Nijeriya gwamnati ta ce ta yi haka ne domin janye tallafin man Fetur, an kuma ba da sanarwa an janye tallafi, sai ga shi a yanzu an dawo da maganarsa har yana lakume kudi haka.

Wannan bayanin nasa yana nuni da cewa za a kara kudin man fetur a nan ba da jimawa ba domin mutanen kasa su shirya kuma an yi haka ne domin su samu alfanu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *