Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ce kungiyar gwamnonin Arewa na aikin ganin an samarwa sarakunan gurbi aiwatarwa a tsarin dokokin kasa don su taka rawa bisa ga tsarin dokar ƙasa.

Tambuwal a wurin kaddamar cibiyar sarakuna da gwamnatin jihar  Delta ta gina a garin Asaba ya ce suna son gudunmuwar sarakuna ta zama cikin daftarin tsarin mulkin ƙasa.
Tambuwal ya ce su gwamnoni suna girmama sarakuna hakan ya sa suke son a samar musu damar da ta dace da su.
Gwamnoni har da shugaban ƙasa suna amfana da ilmi da basirar sarakunan. In ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *