Spread the love
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
 Gwamnatin jihar Zamfara ta ce daga yanzu ba za ta saka ido ta bari wasu na amfani da ‘yan jarida ko yan social media ba wajen ba da rahotannin karya dan gane da sha’anin kalubalen tsaron dake addabar jihar.
 Kwaminan yada labaran jihar, Alhaji Ibrahim Magaji Dosara ne yayi wannan jawabi a lokacin da yake yi wa manema labarai bayani bisa ga matsayar  da gwamnatin Zamfara ta cimma na tsabtace sha’anin rahotannin matsalar tsaro a jihar Zamfara.
 Dosara ya ce, ya kamata duk dan jaridar da ke da wani labari wanda ya shafi kai hari a kauye ko kasuwa ko ina ne to yakamata ya ji ta bakin ‘yan sanda ko ofishin kwamishina ko kuma duk jami’in tsaron da ke iya ba da cikakken bayani kafin rubuta labarinsa.
“Gaskiyar magana ba zamu zura ido muna ganin wasu na rubuta labarai ba tare da sun samu cikakken bayani ga hukumomin da ya kamata su tabbatar da sahihancin labari ba, saboda yin hakan ya sabawa ka’idar aikin jarida.
“Hasalima wasu gurbatattun ‘yan siyasa ne ke  kara hada kai da su domin su ba da rahoton da ba shi da inganci domin dai su kara sa tsoro ga zukatan jama,’a.” inji Dosara.
Da ya dawo bangaren ‘yan social media, Dosara ya ce za ka ga mutum bai san abun da ake nufi da aikin jarida ba sai dai ya dauki waya kawai ya kama posting din abun da bai faru ba don biyan bukatar uwayen gidansu.
“To wallahi a halin da muke ciki duk dan social media da muka ga yayi posting na karya za mu yi amfani da jami’an tsaro mu kama shi sai yayi muna bayanin in da ya samo labarinsa, in ba haka ba zamu kai kotu domin a yi masu hukunci dai dai laifin da suka  aikata”.
 Kwamishinan ya nuna jindadinshi yanda yake samun hadinkan aiki tsakaninsa da wakilan kafafen yada labarai daban daban dake a jihar ta Zamfara, ya ba su tabbacin cewa kofarsa a bude take ga duk wanda ke son karin bayani ga duk labarin da ya samu wanda ke bukatar samun sahihancinsa,
Ya kara da cewa ba shi kadai ba akwai rundunar ‘yan sanda, da rundunar Civil Defence, duk a shirye suke su ba da bayani game da duk labarin da ake neman sahihancinsa.
Taron na manema labarai an yi shi ne a hedkwatar ‘yan sanda Najeriya dake a nan Gusau babban birnin jihar Zamfara, tare da shugabannin yan sanda, da na Civil Defence da kuma wasu daga cikim jami’an gwamnatin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *