Spread the love

Shugaban kasa ya jajan tawa Zamfarawa bisa ga gobarar da ta lashe shaguna 63 a kasuwar Tudun wada.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Wata tawaga ta musammam wadda shugaban kasa Muhammad Buhari ya tura zuwa jihar Zamfara, don jajantawa al’umar jihar kan ibtila’in gobara da ta afkawa ‘yan kasuwan ta isa fadar gwamnatin jihar Zamfara.

Daya yake karbar bakuncin tawagar, gwamna Bello Mohammed Matawalle ya buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya yi la’akari da yadda za’a samar da wani cikakken tsari na aiki, wanda zai ɗore don wanzar da zaman lafiya kamar yadda gwamnatin jihar Zamfara ta fara da nufin kawo ƙarshen ayyukan ‘yan fashi da makami a ƙasar nan.

“Bisa la’akari da abin da ya faru tare da tsagerun Neja Delta, tattaunawa na iya zama mafi kyawun zaɓin kawo karshen rikice-rikicen al’umma, musamman wadanda ke da nasaba da kabilanci ganin cewa ta’addancin ba zai zama wani na daban ba.

“Ina mai sheda maku cewa gwamnatin mu na nan na yaki da wadannan ‘yan fashi da suka ki mika wuya, bayan haka kuma muna gabatar da shirye-shirye daban-daban wanda zai samarwa da matasa da mata da sauran masu rauni sana’ar yi.”

Matawalle ya gode wa tawagar da Shugaban kasar ya turo kan ziyarar kuma ya ce ziyarar ta kara nuna irin son da Shugaba Muhammadu Buhari yake da shi ga al’ummar Jihar Zamfara da kuma kyakkyawan burin gwamnatinsa na kawo karshen matsalolin tattalin arziki da ke addabar mutanen jihar.

Da yake jawabi jagoran tawagar gwamnatin tarayya Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yaba wa matawalle bisa matakin da yake dauka kan matsalar tsaro wanda ya bayyana cewa wannan Gwamnatin cikin dan lokacin da tayi ta sami nasarori masu tarin yawa .

Malami ya bayyana zunzurutun kudi har Naira miliyan bakwai wanda suka bada na kashin kansu don tallafawa ‘yankasuwan, ita kuwa Ministan bada agajin gaggawa, Hajiya Sadiya Umar tace karkashin hukumarta zasu tattauna da Gwamnatin Zamfara don gano irin tallafin da hukumarta zata baiwa ‘yan kasuwan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *