Spread the love

A ranar Lahadi data gabata jam’iyar PDP a Sakkwato ta gudanar yaƙin neman zabɓen shugabannin ƙananan hukumominta a  zaɓen da za a gudanar a 27 ga watan Maris.

Gangamin da aka gudanar a garin Bodinga amadadin yankin Sakkwato ta kudu, Sanata Ibrahim Danbaba Danbuwa wanda shi ne Sanata daya da PDP take da shi a jihar, a jawabin da ya gabatar ya ce akwai buƙatar a haɗa kai a bar zance ɓangaranci dukansu abu ɗaya ne, duk wani mai ƙorafi ya yi hakuri ya kawar da kudirinsa da ba ya da kyau.

“Babu APC a Sakkwato Tambuwal ya kashe ta, a matsayina na Sanata mai wakiltar wannan yanki muna da ƙananan hukumomi 7 shidda daga cikinsu na cire Dange Shuni zan agazawa ‘yan takarar ciyaman da dubu 500 kowanensu, zan baiwa karamar hukuma miliyan biyu, shugabannin yanki miliyan daya na jiha miliyan biyu.” a cewar Sanata Danbaba Dambuwa.

A jawabin da tsohon shugaban jam’iyar Alhaji Ibrahim Milgoma ya gabatar ya ce kar Sanata ya ce ya ɗoki yankinsa kawai kamata ya yi gaba daya domin yana iyawa.

Shugaban jam’iyar na jiha Alhaji Bello Aliyu Goronyo a jawabinsa ya ce ya goyi bayan Milgoma don su ba su son a nuna bangaraci don haka suke kira gare shi da baiwa kowa.

Managarciya ta dubi wannan kalaman nasu a matsayin watsa masa kasa ne a ido domin shi kadai ne wanda ya bayyana gudunmuwarsa a fili don tallafawa tafiyar da jam’iyar. Mi zai hana a gode masa da jawo hankalin wasu jagorori dake wani yanki su yi koyi da shi har su wuce abin da ya yi.

Sanata Danbaba agazawa ya ce zai yi abin da ke nuna abin da zai yi ana buƙatarsa don haka  godiya yake jira ba cin gyaran abin da ya yi ba, akwai buƙatar jagororin su sauya lalensu kowace hoɓɓasa mutum ya yi komi ƙanƙantarta a yaba masa don ƙara ƙwarin guiwa ga abin da yake ganin dama ne ba dole ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *