Kananan kasuwanci kusan miliyan 40 ake da su a Nijeriya—–Hukumar kula da ingancin kaya ta Nijeriya

 

 
Daga Muhammad M. Nasir
 
Shugaban hukumar kula ingancin kaya a Nijeriya(SON) Malam Faruk Salim ya ziyarci Sakkwato domin fara ginin katafaren ofis na hukumar a yankin Sakkwato wanda zai kula da jihohin Zamfara Kebi da Katsina.
Shugaban a lokacin da ya ziyarci fadar gwamnatin jiha ya ce gwamnatin tarayya tana son ta kara samar da kudin shiga ne ta hanyar kara inganta kayan da ake amfani da su a kasar.
Malam Faruk ya ce a Sakkwato akwai kananan kasuwanci da ake yi sosai don haka muke son taimaka musu a inganta su in  za a  fitar da su waje ba a shakkar idon kowa shi ne babban burinmu.
“A kididdigar da aka yi akwai kasuwanci kusan miliyan 40 a Nigeriya kuma akwai sana’oin a Sakkwato a haka muka ga dacewar samar da ofis a yankin tare da yin dakin gwaje-gwaje da za a rika duba kananan kasuwancin.” a cewarsa.
Salim Ya ce hukumarsu ba ta yarda a shigo da kayan da ba su da inganci ba kuma duk jami’insu da suka kama ya hada baki da wasu a yi rashin gaskiya za su kore shi a kuma gurfanar da shi gaban kuliya.
Ya yi karin bayani kan cewar ba wuraren gwaji a Arewa ya ce a duk in da ofis na su yake akwai dakin gwaji dauke injina, sai babban dakin ne yake a Lagos, amma sun fara shirin samar da irinsa a Sakkwato tare da hadin kan gwamnatin jiha.
Gwamnan Sakkwato ya kafa harsashen ginin ofis a kan hanyar filin jirgin sama a birnin Sakkwato.
 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *