Spread the love
Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya yi alkawarin tabbatar da hadin kai a tsakanin mambobin  APC a duk faɗin Nijeriya.
Gwamnan ya yi wannan bayanin ne lokacin da yake yi wa manema labarai ƙarin bayani a hedikwatar jam’iyyar dake Abuja bayan an ƙaddamar da su a matsayin kwamitin tuntuɓa da tsare-tsare, wanda shi ne shugaba.
A cewarsa Jam’iyyar APC a ƙarƙashin kwamitinsa zai yi kokarin dawo da mutanen da suka bar jam’iyyar sannan kuma za ta nemi sabbin mambobin a duk fadin kasar.
“Mu a matsayinmu na Jam’iyya kuma da sabon nauyin da aka ɗora mana a matsayinmu na kwamiti, za mu tabbatar da  haɗin kan wannan  jam’iyya ba a gurgunta shi ba. Kuma za mu tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin mambobinmu a dukkan jihohi 36.” a cewar Badaru
“Wasu mutane an ɓata musu, kuma sun bar Jam’iyyar saboda wanannan dalili, wasu mutane ma suna da kyakkyawar niyya ga kasar amma ba sa cikin Jam’iyya. Don haka, aikinmu a wannan kwamiti zai kasance ne na dawo da wadanda suka fice daga Jam’iyyar da kuma jan hankalin sabbin mambobin da ke da kyakkyawar niyya ga Nijeriya.” in ji Badaru
Ya sanar cewa a Yuni ne za su gudanar da babban taronsu na ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *