Spread the love

Gwamnan Zamfara ya kalubalanci yan siyasar Zamfara da su rantse da Alkur’ani mai girma inba suda hannu wajen rashin tsaro.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnan Zamfara Bello Mohammed ya kalubalanci ‘yan siyasa da manyan jihar Zamfara da su yi rantsuwa da Alkur’ani mai girma in har sun tabbatar da cewa ba su da hannu a matsalar rashin tsaron da ya addabi jihar.

Matawalle ya yi wannan maganar ne a lokacin da aka karrama shi da sarautar Khadimul Qur’an, na biyu a fadin Najeriya, wanda Cibiyar mahardata Kur’ani ta kasa ta bashi, a garin Gusau fadar gwamantin jihar.

Cibiyar mahardatan dai ta ce ta yi mashi wannan karramawar ne bisa ga la’akari da irin gudunmuwar da yake bayar wa ta haujin kare littafen Allah, da kuma mayarda hankali wajen ci gaban addinin musulunci.

Matawalle ya yi na’am da wannan karramawar inda yasha alwashin ci gaba da taimakawa ga dukkan abin da ya shafi addinin musulunci, ya kuma jaddada shirin sa ne ganin cewa an samu dauwamamen zama lafiya a jihar Zamfara.

Gwamnan wanda ya nuna jin zafinsa bisa ga irin yanda wasu ke siyasantar da harka tsaro, ya rantse da Allah baya da hannu kuma bai san wani wanda ke da hannu wajen rura wutar rashin tsaron dake addabar jihar ba.

A don haka ya ƙalubalanci ‘yan siyasa da manyan jihar zamfara daga bakin janar Ali Gusau har tsofaffin gwamnoni kama daga Yariman Bakura har ƙasa da su fito su rantse kamar yanda yayi cewa ba su da hannu a wannan matsalar.

Kuma nan take ya ba da umurnin cewa duk wanda ke cikin gwamnatinsa mai fada a jiya kama daga kwamishinoni har manyan sarakuna da su fito su yi rantsuwa cewa ba su da hannu a matsalar tsaron da ta dabaibaye jihar, ta hana ci gaba.

“Idan kowa ya rantse ba ya da sa hannu cikin wannan matsalar, to shi zai sa jama’a su san ko suwaye ke rura wutar wannan matsalar, kuma wallahi da sai kunga an mutu da yawa, koda zaman lafiya zai dawo muna.

“Wannan matsalar takai kul wallahi, saboda haka kowa ya rantse kamar yanda na rantse, amma baya yiwuwa muna iya kokarin mu amma wasu na kawo muna cikas.

“A matsayi na na shugaban tsaron wannan jihar ta Zamfara zan yi duk abin da ya kamata domin in kawo ma mutanen jiha ta zaman lafiya mai ɗorewa, domin kowa ya samu sukunin zuwa wajen neman abinci kamar yanda aka saba a can baya, ba da jin tsoron komi ba.” inji Matawalle.

Daga ƙarshe yayi kira ga al’ummar wannan jihar dasu hada kansu domin su kalubalanci makiya jihar su a duk inda suke. Domin magance matsalar tsaro bata mutun daya ce ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *