Spread the love
Majalisar Tuntuɓa Da Haɗaka ta Arewa (ACSC) ta nuna rashin jindaɗinta bisa ƙaruwar ayyukan ta’addanci a Lardin Arewa musammam a fannin ilimi da ake son kassarawa.
A hakikanin gaskiya, ba ƙasa ko al’ummar da za su sami duk wani cigaban Siyasa, Tattalin arziki da samun ‘yancin gudanar da harkokin addini a cikin irin wannan yanayi na tashin hankali, don haka bamajin daɗin abin da ke faruwa a Arewa. “Bama iya barci saboda baƙin cikin halin da ilimi da tattalin arziki suka shiga yayin da ta ko’ina ake kaiwa makarantu hari  wannan babban abin damuwa ne.
“Don haka, mu a ACSC Muna kira Gwamnonin Arewa da su kawar da banbancin dake tsakaninsu domin su haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen kawo ƙarshen ayyukan ‘yan Ta’adda a Arewa.
“Haka zalika, ya zama wajibi  a Samar da hukumci mai tsauri a kan masu aikata ta’addanci,  muna yabawa da ƙoƙarin da hukomin tsaro suke yi don ganin an kawo ƙarshen ayyukan Ta’addanci a Arewa.
“Bugu da kari, muna kira a gare su da su dage, su mayar da hankali kan ayyukansu, kuma su girmama dokokin ƙasa, su saka kishin ƙasa a lokacin aiki, kana su kiyaye dokokin kare haƙƙin Ɗan Adam a kan mutanen da babu ruwansu akan abinda ke faruwa na ta’addanci a yankunan su.” a cewar Shugaban hadakar ta kasa Injiniya Dakta Haris Jibril.
Ya  jajantawa Mai Martaba  Sarkin Birnin Gwari  da Gwamnan Jihar Benue Mista Samuel Otom bisa iftilain da ya faru.
Haka kuma ya  Jajantawa  Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi  Sa’ad Abubakar  da Gwamnatin Tarayya,  bisa rasa rayuka da dukiyoyi da aka yi a Arewa, kuma da yin addu’ar fatan Allah ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *