Spread the love
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Da maraicen yau ne aka yiwa gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle allurar rigakafin cutar korona a fadar gwamnatin jihar dake a garin Gusau.
Da yake bayani ga al’ummar jihar zamfara jim kadan ba yan anyi masa allurar, gwamna Matawalle ya ce, shi ya karbi tashi allura sauran ma’aikatansa da kuma manya manyan yan siyasa dake fadin jihar.
Hakama yayi kira ga al’ummar wannan jihar masu bukata da su fito ayi masu allurar, kuma ba’a biyan ko kwabo kyauta ake yinta, ya kara da cewa za su yi yekuwa ga al’ummar jihar dan gane da muhimman cin rigakafin korona.
Daga cikin mukarraban gwamnatin da aka yi wa allurar ta korona tare da gwamna sun hada da, shugaban majalisar dokokin jihar  Alhaji Nasiru Mu’azu Magarya, da mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Dakta  Bashir Maru, daga baya za’a ci gaba daga inda aka tsaya.
Da yake yi wa manema labarai bayani bayan yayi wa gwamna da sauran mukarraban gwamnatin allurar, kwamishinan lafiya na jihar Alhaji Yahaya Muhammed Kanoma
  Ya bayyana cewa jimillar mutane 27,960 ne za su karbi alluran a jihar inda ya kara da cewa, za a yi allurar rigakafin ne tun daga yara ‘yan shekaru 18 zuwa sama a duk fadin jihar.
Kwamishinan ya kara da cewa za’aci gaba da yin allurran har sai lokacin da aka kammala yima dukkan mutanen jihar ta zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *