Spread the love

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ce jam’iyar APC a Nijeriya ta dauki hanyar rushewa a Nijeriya ba a Sakkwato kadai ba da suka kasa shiga zaben kananan hukumomin don sun san ba su da nasara.

Gwamna Tambuwal ya yi wannan kalami ne a wurin taron kaddamar da ‘yan takarar shugabannin kananan hukumomi na jam’iyar PDP a yankin Sakkwato ta gabas a ranar Assabar da ta gabata.

Jam’iyar APC sun kauracewa zaben ne kan zargin ba za a yi masu adalci ba, kuma akwai dokokin zabe da hukumar zabe ta jiha ta karya.

Tambuwal ya ce sun janye ne kawai kan rikita-rikitar da ta mamaye su domin jam’iyar APC ba ta da abin nunawa a kasa tun sanda ta shigo mulki a 2015.

Taron ya gudana ne a karamar hukumar Gwadabawa wadda tana cikin kananan hukumomi da mahara ke shigowa don haka Gwamna ya yi kira ga mutane su baiwa jami’an tsaro hadin kai domin dawo da zaman lafiya a yankin.

Tambuwal ya ce a jihar Sakkwato gwamnatinsa na gudanar da aiyukka a kowane lungu da sako na jihar akwai bukatar al’umma su rika kula da aiyukka da gwamnati ta yi masu domin cigabansu da jiha baki daya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *