Spread the love

 

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

A jiya juma’a 18 ga watan aka kaddamar da gasar Karatun Alƙur’ani ta kasa a Convacational Arena da ke jami’ar Bayero ta Kano, a duk shekara akan zaɓi jiha domin gudanar da ita a jihohin Nijeriya.

Musabaƙar wacce ita ce karo na 35, ana gabatar da ita ne duk shekara da Jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto ke shirywa.

Gwamnan jihar Kano Dakt Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne suka zama manyan baki na musamman, yayin da yan takara da manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan suka halatta,

‘Yan takara sun fara fafatawa a yammacin jiya da karfe 4 na yamma, inda aka bude daga ‘yan takara izifi 10. sannan za’a yi bikin rufe gasar a ranar Asabar ta sama wanda ya yi daidai da 27 ga watan da muke ciki.

Musabaƙar tana gudana duk shekara domin ganin an zaburar da matasa masu son Ƙur’ani su iya karanta shi don shi kaɗai ne hanya ɗaya ta tsira.

Musabaƙar tana da  matuƙar muhimmanci ga addinin musulunci musamman a wannan yanayin da ake ciki da musulmai ke ƙoƙarin kare littafin na Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *