Spread the love

 

Yawan maras aikin yi masu zaman kashe wando ya karu a Nijeriya cikin zangon karshe na shekarar 2020 abin da ya sanya kasar ta zama ta biyu a duk duniya da ke da marasa aikin yi.

A duk Afrika tafi yawan mutane in da take da al’umma sama da miliyan 200, a zangon shekarar daata gabata yawan marasa aikin yi a Nijeriya kashi 27.1 ne amma a zango na hudu sai gashi ya kai kashi 33.3 kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa(NBS) ta bayar.

A cewar NBS rashin aikin yi ya ragu daga  kashi 28.6 zuwa 22.8, in ka hada marasa aikin yi da rashin aikin yi wuri daya a zango na hudu na shekarar data gabata ya kai kashi 56.1

Wannan kididigar ta nuna jihar Imo ce tafi yawan marasa aikin yi a Nijeriya da kaso 56.6 sai jihar Adamawa ta biyo bayanta da kashi 54.89

In ka hada rashin aikin yi da marasa aikin yi a wuri daya Imo nada kaso 82.5 sai Jigawa da kashi 80.

Jihohin da suke saukin wannan matsalar Ogun nada kashi 26.2 sai Sokoto da kashi 33.7.

Hakan ke nuna akwai bukatar gwamnatin Nijeriya da jihohi su yi wani abu da zai taimaki matasan kasa domin tsamo su ga halin rashin aikin yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *