Ahmad Lawan Ya Buƙaci ƙasar Saudi Arebiya ta dawo da ‘yan Najeriya Dubu Goma Dake Tsare  A Kasar
Daga M. A. Umar, Abuja
Shugaban majalisar dattijai, Dakta Ahmad Lawan ya bukaci gwamnatin kasar Saudiya da ta taimaka wajen maido da ‘yan Najeriya sama da dubu goma da ta ke tsare da su a kasar.
Lawan yayi wannan kiran ne yayin da jakadan Saudiya a Najeriya Faisal Eebraheem Alghamdi ya kai masa ziyara a ofishinsa dake Abuja.
Shugaban majalisar ya shaida ma jakadan cewa dubban yan Najeriya suna tsare a kasar Saudiya, yana mai cewa gwamnatin Najeria ta dauki matakan cigaba da wayar da kan yan kasar ta masu zuwa aikin Ibada a kasar akan bukatar dawo wa gida da sun gama abin da ya kai su na Ibadah.
Ya ce gwamnatin Najeria na yunkurin kwashe dukkanin ‘yan kasar ta dake zaune a Saudiya ba bisa ka’ida ba don dawo da su gida, inda ya bukaci gwamnatin kasar Saudiya ta taimaka ma Najeria a wannan aiki.
Ya ce, “a yanzu haka muna da yan Najeriya sama da dubu goma da ba su da rijista kuma suna tsare a gidajen yari a Saudiya, bukatar mu itace mu fito da su, su dawo gida.
Lawan ya bada tabbacin cewa kyakykyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu za ta cigaba da dorewa.
Ezrel Tabiowo, mai taimakawa shugaban majalisar akan aikin jarida ne ya fitar da sanarwar a wata takardar manema labarai yammacin alhamis din makon nan a Abuja.
Inda ya kara da cewar shugaban majalisar ya kuma roki gwamnatin Saudi Arabia da ta yi amfani da mukaminta na mai fada a ji a kungiyar kasashe masu albarkatun man fetur watau OPEC don kara ma Najeria yawan adadin man fetur da zata iya hakowa a duk rana.
Yin haka  a cewar sa, zai ba Najeriya damar cimma bukatun ta na samar da kayayyakin more rayuwa ga jama’ar ta da yawan su kullum ke bunkasa.
Ya ce, adadin gangar mai miliyan 1.5 da aka ware ma Najeriya a kullum yayi karanci duba da yawan jama’ar ta da kalubalen samar da kayayyakin more rayuwa da take fuskanta.
Ya ce Najeriya ta na samun kashi 90 na kudeden kasashen waje daga man fetur da take saidawa ne, don baka tana bukatar karin yawan man fetur da za ta fitar.
Tunda farko, jakadan kasar Saudiya a Najeriya yace ya kai ziyarar ne don kara dankon zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *