Spread the love

Gwaman jihar Bauchi Bala Muhammad ya ce jam’iyarsu ta PDP ce ta samu nasara a zaben shugaban kasa na 2019.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a APC da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar a PDP  su ne kan gaba da suka gwabza a zaben.

Hukumar zabe ta kasa ta aiyana jam’iyar APC ce ta samu nasara a zaben, abin da Atiku da jam’iyarsa suka kalubalanta a kotun kolin kasa abin da ba su yi nasara ba a kai.

Gwamnan a lokacin da yake bayani a shirin gidan talabijin na Chanels  ‘Politics Today’ ya zargi aringizo aka yi masu tsakanin hukumar zabe da jami’an tsaro.

Ya ce mutanen Nijeriya sun ga abin da ya faru a lokacin zaben na 2019 kuma sun koyi darasi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *