Spread the love

‘Yan bindiga sun kai hari a Kasuwar ‘Yar tasha sun kashe mutun 1, sun kwashe dukiya da kone rabin Kasuwar a Zamfara.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Wasu gungun mutane fauke da bindigogi waɗanda ake kyautata zaton ‘yan bindigar da suka bijire wa shirin sulhun da gwamnatin Zamfara ke yi, sun kai wani mummunan hari a Kasuwar ƙauyen ‘yar tashar Sahabi dake karkashin gundumar Dansadau a karamar hukumar mulkin Maru dake jihar Zamfara.

Maharan dai sun samu nasarar babbake rabin kasuwar da kuma sa ‘yan Kasuwar asarar dukiyar da ba’asan adadin ta ba kuma sunyi a won gaba da duk abun da ke da amfani a cikin kasuwar ƙauyen na ‘Yar Tasha Sahabi.

Kamar yanda managarciya ta samu labari ga wani wanda ya ga yanda lamarin ya faru, amma yace kada a saka sunansa, ya ce ‘yan bindigar da suka shiga kasuwar waɗanda yawansu yakai kimanin su 100 sun cigaba da harbi ta sama don su kori ‘yan kasuwa bayan kowa na gudun tsira su kuma sai suka cigaba da kwasar dukiyar jama’a.

A tabakinsa, duk mutane sun shige cikin gidaje domin su tsira da rayuwarsu, amma dai duk da haka sun harbe wani mutun kuma anan take ya rasu, suna cikin wannan ta’asar sai ga ‘yan sandan karta kwana dalilin ganin su ne yasa maharan janyewa daga cikin kasuwar .

A lokacin hada wannan wannan labarin an yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun yansandan jihar Zamfara SP Muhammed Shehu, amma abun ya cutura inda duk wayoyin sa a kashe suke.

Idan baku mantaba duka yau kwana biyu da yin ta’addanci a kauyen Kabasa dake gundumar Magami karamar hukumar mulkin Gusau inda suka kashe soja uku, dawasu mutun biyar dake cikin garin, sannan kuma suka ƙona motar sojoji guda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *