Spread the love

Jam’iyar PDP mai adawa a Nijeriya ta zargi jam’iyar APC da jagororinta sun yi sama da fadi da kudi wanda yawansu yakai naira Tiriliyan 15 a lalitar gwamnati, kan haka sun shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kokarin kwato kudin da aka sace a gwamnatinsa.

A fili yake yadda jam’iyar APC ke kokarin rufe wannan badakalar da suka tabka abin da mutanen Kasa ba za su aminta da shi ba kenan sai an binciki shugabannin APC a dawo da kudin kasa domin amfanin mutanen Nijeriya.

Sakataren yada labarai na jam’iyar PDP Kola Ologbondiyan ne ya fitar da wannan bayani a wata takarda da ya sanyawa hannu ya ce hakan ya nuna wannan kazamar satar da APC ta yi ne ya kara jefa kasar cikin karin rashin aikin yi da wahala da rashin kayan more rayuwa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *