Spread the love
Daga M. A. Umar, Abuja.
Majalisar dattawa tayi nazari da amincewa da kudurin dokar da zai kara samar ma Najeriya kudaden kasahen waje ta hanyar fitar da mankade zuwa kasashen waje.
Kudurin dokar da akayi ma karatu na biyu a ranar Talata yana kokarin kafa majalisar habbaka mankade ta kasa, watau National Shea Development Council.
Sanata Muhammad Enagi Bima (APC- Niger) da ya gabatar da kudurin, yace ana bukatar kafa majalisar ne don samar da tsari akan harkar mankade da dawowa da wuraren noman sa da suka lalace da kafa sababbi da kuma samar da aiki  yi ga mata dake yankunan karkara.
Bima yace Allah ya albarkaci Najeriya da itatuwa masu tarin yawa dabam-dabam da suka hada da koko, yazawa, rogo, mankade, auduga, rogo da sauran su.
Yace a duk cikin wadannan itatuwan, shukawa da kula da itacen kadanya da ke samar da mankade aka fi yin watsi da shi.
Yace Najeriya ke samar da kashi 62 da ya yi daidai da metrik ton 370,000 a shekara daga cikin metrik ton 600,000 da aka kiyasta ana amfani da shi a duniya.
A  cewar sa, idan aka inganta harkar noman kadanya ta hanyar kyakykyawan tsari da saka jari, bangaren zai ba gwamnati gudummuwa wajen kokarin ta na kara hanyoyin inganta tattalin arziki.
Yace ana bukatar mankade da kwatankwacinsa ya kai dala bilyan hudu a duniya tare da kiyasin zai kai dala bilyan 10 a shekarar 2030.
Bima yace babbar gajiyar mankade ga Najeriya shine samar da kudaden kasashen waje ga gwamnati, samar ma mata aikin yi, samar da ikin yi, bunkasa masana’antu da samar da kayan more rayuwa a kauyuka.
Tuni dai shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya mika kudurin dokar ga kwamitin majalisar akan aikin gona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *