Spread the love

 

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari Abubakar ya ja kunnen gwamnatin jihar ta Zamfara da ka da su sa siyasa ga sha’anin taɓarɓarewar tsaron da ya addabi jihar.

Tsohon gwamnan ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa dake Mafara, hedikwatar ƙaramar hukumar mulki Talata Mafara jihar Zamfara.

Ya ce mai makon zargin cewa akwai ‘yan jam’iyyar adawa dake rura wutar rikici kamata yayi a dukufa wajen gano kan zaren warware matsalar.

Ta bakin shi lokacin da yake mulkin jihar shi bai zargi kowa ba, ya dauka cewa abu ne wanda Allah ya kawo, kuma shi kadai zai yi maganin shi.

Tsohon gwamnan daga nan ya shawarci gwamnati mai ci yanzu da su ci gaba da hada hannu da gwamnatin tarayya domin cimma gurinsu na ganin cewa an samu zaman lafiya mai ɗorewa a fadin jihar da kuma sauran jihohin da abun ya shafa.

“Rashin tsaro a wannan ƙarnin ya zama ruwan dare game duniya, ko wace ƙasa tana da tata matsalar rashin tsaro, abun da yafi a gare mu shi ne mu haɗa hannu waje ɗaya, kuma mu ba da gudunmuwa domin mu ceto mutanen mu dake fama da wannan iftila’in.

“Ya kama ta mu aje duk wata adawa, ko siyasantar da wannan bala’i da ke laƙume rayukkan mutane da kuma sasu hasarar dukiyoyi. Ina iya tunawa satin da ya gabata mun hadu da shugaba Muhammadu Buhari wajen taron da akeyi na harkar tsaro a fadar gwamnati.

“Dukan mu mun hadu ba maganar banban cin siyasa ko bangaran ci, inda muka cimma matsaya cewa zamuyi aiki tare da gwamnatin tarayya domin mu tabbatar da an samu zaman lafiya ba wai a zamfara kadai ba, a, a duk fadin kasar tamu ta Najeriya.”Inji Yari.

Daga karshe ya shawarci gwamna Bello Matawalle da cewa, ya kamata ya yasa hikima wajen fuskantar wannan sha’anin na rashin tsaro a jihar Zamfara, ya kuma yi wa duk shawarar da za’a bashi karatun ta natsu ta yanda zai iya murƙushe duk dan ta’addan da baya son zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *