Spread the love
An jima ana raderadin an samu wata alakar siyasa tsakanin Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela Dakta Abdullahi Balarabe Salame a yanzu  dai ta fito fili akwai wannan alakar da aka yi wa lakabi da siyasa ba da gaba ba.
Dan majailsar a yau Litinin ya gayyaci gwamna Tambuwal bukin bude asibitin da ya gina a mazabar Mammande dake karamar hukumar Gwadabawa wadda ta kwashe shekara biyar ana ginawa.
Salame a jawabin da ya gabatar kafin hannunta makullan asibitin ya bayyana Tambuwal a matsayin mutum mai son jihar Sakkwato da yin siyasa ba da gaba ba.
Ya yaba gwamna da ya karbi gayyatarsa da turo ma’aikatan lafiya a asibitin, in da ba a yi hakan ba da aikin ba ya da wani amfani zai koma wurin hutawa ne kawai ba asibiti ba. a cewarsa.

A wata uku da suka wuce Managarciya a wata fira da ta yi da Salamen ya ce bai gamsu da yanda ake tafiyar da mulki a Sakkwato ba sam-sam har a baya ma, ba’a lokacin Tambuwal kadai ba, an bar Sakkwato baya sosai.

Dakta Abdullahi Salame ya nuna son cigaban jiha ne ya sanya ya rungumi Tambuwal a yanzu domin ciyar da jihar gaba ta hanyar aiwatar da wasu aiki da yankin nasa ke bukata kamar kammala gyaran asibitin Salame domin rashinta na jefa mutanen yankin cikin matsala da wahalar rayuwa in hadari ya samu na mota ko mashin ko wata rashin lafiya.
Managarciya na kallon wannan matakin na Salame neman mafita ne kawai na siyasa ganin yanda jam’iyarsa da yake ciki a yanzu ta APC da wahalar gaske ya samu gurbi matukar ba lissafin da ake ciki yanzu ya sauya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *